Yadda Zaku Inganta Tsaron Website Dinku

security

January 1, 2025

Tsaron website yana da matuƙar muhimmanci domin kare bayanai da hana masu kutse samun damar kutsawa cikin site dinku suyimuku barna.

Ga wasu matakai da zaku bi:

Yi Amfani da HTTPS (SSL Certificate)

Tabbatar da cewa website dinka yana amfani da HTTPS maimakon HTTP. Wannan yana tabbatar da bayanai suna tafiya cikin tsaro tsakanin mai amfani da server.

Sabunta Software Dinka Akai-Akai

Idan kuna amfani da CMS (kamar WordPress) ko kuma custom code, sabunta software yana taimakawa wajen rufe ɓoyayyun barazanar tsaro.

Idan kuna amfani da wordpress Kutabbatar da kuna sabunta (updating) din themes da plugins dinku akia akai domin wani lokacin idan akayi updating din theme ko pluging akwai wasu bug da ake ganowa a magancesu to idan baka sabunta nakaba zai zamo cewa kai baka da kariya za’a iya yimaka kutse ta wannan plugins din don haka wannan yana da matukar muhimmanci.

Haka ida idan kana amfani da script ko custom code ka tabbata kana updating dinsa akai akai domin tabbatar da tsaron site dinka.

Yi Amfani da Kalmar Sirri Mai Ƙarfi

Ku tabbatar kuna amfani da kalmomin sirri masu ƙarfi da haɗakar lambobi, haruffa manya da ƙanana, da alamomin musamman.

kamar:

%AGE$5Ecvi3eSCid

Domin yin amfani da kalmar sirri mai karfi yana kareka daga masu kutse kai tsaye domain masu kutse wani lokacin sunayin amfani da numbar wayarka wajen yin kutse, idan suka zu kutse site dinka zasu sami email dinka idan sun samu to abu na farko da zasu fara gwadawa a matsayin kalmar sirrinka shine numbar wayarka idan kana amfani da numbar waya amtsatsayi kalmar sirri to ka daina yi amfani da kano host domain yin ganarating kalmar sirri mai karfi tanan https://tools.kanohost.com/ .

Yi Amfani da Firewall

WAF (Web Application Firewall) na taimakawa wajen kare website daga harin SQL injection, XSS, da sauran irin waɗannan hare-haren.

Kare Admin Panel
  • Canza URL ɗin admin panel daga tsohon adireshi kamar /admin zuwa wani abu na musamman.
  • Ƙara ƙarin matakin tsaro kamar 2FA (Two-Factor Authentication).
Takaita Permissions na Files

Ka tabbatar cewa permissions na files da folders ba su yi yawa ba. Alal misali, ka sa 644 ko 600 don files, da 755 ko 700 don folders.

Yi Backup Akai-Akai

Ajiye backup na website dinka a wuri mai tsaro. Wannan yana taimakawa wajen dawo da website idan aka samu matsala

Kare Tsarin Database
  • Yi amfani da sunayen tables na musamman maimakon tsofaffi kamar users ko admin.
  • Kare SQL queries dinka daga injection ta amfani da prepared statements.
Saka Tsaro akan Uploads

Idan website dinka yana bada damar upload, ka takaita nau’in fayilolin da za a iya ɗora. Ka kuma bincika fayilolin kafin su shiga server.

Yi amfani da Tools don Monitoring

Yi amfani da kayan aikin kamar Google Search Console, Sucuri, ko SiteLock don lura da yanayin tsaro na website dinka.

Insha allah idan kuka bi wadannan matakan zaku kare site dinku daga kutse ga yan fashin online, kuma mu a kanohost duka wadannan tsare tsaren muna dasu kudai ku garzaya kanohost domain siyan web hosting ko domains a farashi mai sauki dannan nan.

Recent Courses

You May Also Like…

0 Comments

Submit a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Pin It on Pinterest

Share This

Share this post with your friends!