Akwai HTTP Status Codes da yawa da ke nuna matsaloli daban-daban a website. Ga cikakken bayani game da 404, 500, da sauran su, da dalilan da ke jawo su, da yadda ake magance su.
🔵 100 – (Informational Responses)
Wadannan codes din yana nuna cewa server tana aiki da kyau kuma tana jiran karin bayani daga client.
100 – Continue
🔹 Ma’ana:
-Server ta karɓi farkon request kuma tana jiran karin bayani daga client.
-Ana amfani da 100 Continue don large file uploads ko chunked requests
🔹 Misali:
-Idan browser yana aikawa da large file upload, zai iya amfani da 100 Continue kafin ya gama aikawa.
🔹 Yadda ake amfani da shi:
-Wannan yawanci yana faruwa a background kuma ba sai an yi handling dinsa ba idan kai ba developer bane da ke aiki da HTTP request directly.
🟢 200 – (Success Responses)
Wadannan codes yana nuna cewa request ɗin da aka aika ya tafi daiadai kuma an sami amsa mai kyau daga server.
200 – OK
🔹 Ma’ana:
-Server ta karɓi request kuma ta mayar da respond na nasara.
-Wannan shi ne a matsayin da ake so a shafukan yanar gizo da APIs.
🔹 Misali:
-Idan ka bude wani shafi a browser kuma komai yana aiki daidai, za a mayar da 200 OK.
-Idan API ya mayar da sakamakon query (e.g., user data), zai dawo da 200 OK.
🔹 Yadda ake amfani da shi:
Ba a bukatar gyara idan 200 OK ne, yana nuna komai yana aiki daidai.
201 – Created
🔹 Ma’ana:
-Server ta ƙirƙiri wani sabon abu cikin database ko wani wuri kuma an sami nasara.
-Wannan yawanci ana amfani da shi a RESTful APIs.
🔹 Misali:
Idan ka aika request don ƙirƙirar sabon user, kuma an yi nasara, za a dawo da 201 Created tare da sabon user ID.
🔹 Yadda ake amfani da shi:
A Laravel API, idan kana ƙirƙirar resource, zaka iya yin:
return response()->json(['message' => 'User created'], 201);
🟡 300 – Redirection Responses
Wadannan codes suna nuna cewa akwai wani canji ko turawa daga wani adireshin zuwa wani.
301 – Moved Permanently
🔹 Ma’ana:
-Shafin da ake so ya koma wani wuri na dindindin.
-Duk requests daga yanzu za su tafi sabuwar adireshi.
🔹 Misali:
Idan ka canza adireshin website daga http://example.com zuwa https://example.com, zaka iya amfani da 301 Redirect.
🔹 Yadda ake amfani da shi:
Idan kana son redirect daga HTTP zuwa HTTPS a .htaccess:
RewriteEngine On
RewriteCond %{HTTPS} !=on
RewriteRule ^ https://%{HTTP_HOST}%{REQUEST_URI} [L,R=301]
Wannan yana tabbatar da cewa duk wanda ya shiga HTTP, zai tafi HTTPS.
302 – Found (Temporary Redirect)
🔹 Ma’ana:
-Ana turawa zuwa wani wuri, amma wannan turawar ba na dindindin ba ne.
-Clients (e.g., browsers) zasu iya ci gaba da amfani da tsohon adireshin idan sun sake request.
🔹 Misali:
Idan kana da wani maintenance mode kuma kana son redirect users zuwa wani wuri na ɗan lokaci.
🔹 Yadda ake amfani da shi:
Idan kana son redirect ɗan lokaci a Laravel: return redirect(‘new-page’)->with(‘message’, ‘Temporary Redirect’);
return redirect('new-page')->with('message', 'Temporary Redirect');
Idan kana amfani da .htaccess:
Redirect 302 /old-page.html /new-page.html
304 – Not Modified
🔹 Ma’ana:
-Wannan yana nuna cewa shafin bai canza ba tun da client ya duba shi.
-Browser zai yi amfani da cached version domin rage bandwidth da loading time.
🔹 Misali:
Idan browser yana da cached version na wani shafi, zai aika request yana cewa:
If-Modified-Since: Wed, 21 Oct 2023 07:28:00 GMT
Idan server ya ga cewa babu wani sauyi a shafin tun wancan lokaci, zai mayar da 304 Not Modified maimakon sake aika cikakken shafin.
🔹 Yadda ake amfani da shi:
Idan kana so browser caching ya yi aiki da kyau, zaka iya sa cache control a cikin .htaccess:
<IfModule mod_expires.c> ExpiresActive On ExpiresByType text/html "access plus 1 month" ExpiresByType image/jpeg "access plus 1 year" </IfModule>
🔎 Taƙaitaccen Tebur akan HTTP Codes
Code | Ma’ana | Dalili | Misali |
---|---|---|---|
100 | Continue | Server yana jiran karin bayani | Large file upload |
200 | OK | Request ya yi nasara | Duk wani shafi da ke aiki daidai |
201 | Created | Sabon abu an ƙirƙira | Sabon user an ƙara a database |
301 | Moved Permanently | Shafi ya koma wani wuri har abada | HTTP → HTTPS redirect |
302 | Found (Temporary Redirect) | Redirect na ɗan lokaci | Maintenance mode |
304 | Not Modified | Shafi bai canza ba tun ƙarshe | Browser caching |
Wadancen da muka kawo da farko basu da wata matsala, Sanan ga danda idan ka gansu to suna nuna cewa akwai wata matsala dake faruwa
🔴 400 – Client Errors (Matsaloli daga bangaren mai ziyarta)
404 – Not Found
🚨 Dalilai:
-Shafin da kake nema ba bushi.
-URL ko adireshi bai daidai bane.
-Fayil ɗin da ake so ba ya nan a cikin server.
✅ Yadda ake magancewa:
-Tabbatar da cewa adireshin da kake amfani da shi daidai ne.
-Duba idan fayil ɗin yana nan a cikin public_html ko public (idan Laravel kake amfani da shi).
-Idan kana amfani da Laravel ko .htaccess, tabbatar da cewa routes suna daidai.
403 – Forbidden
🚨 Dalilai:
-Babu izini (Permission) don shiga shafin.
-Ana hana shiga wasu fayiloli ko manyan fayiloli.
.htaccess yana hana wasu accessing din wasu files din da aka sa.
✅ Yadda ake magancewa:
Canja permission:
chmod -R 755 public_html
Idan Laravel kake amfani da shi:
chmod -R 775 storage bootstrap/cache
405 – Method Not Allowed
🚨 Dalilai:
-Aikace-aikacenka (API ko Laravel) yana bukatar GET, POST, PUT, DELETE, amma an aika request da method ba daidai ba.
Misali: Idan route ɗinka yana karɓar POST, amma kai ka aika GET.
✅ Yadda ake magancewa:
Duba routes/web.php ko routes/api.php don tabbatar da daidaiton method.
🔴 500 – Server Errors (Matsaloli daga bangaren server)
500 – Internal Server Error
🚨 Dalilai:
-Akwai kuskure a cikin PHP/Laravel code.
-.htaccess yana da matsala.
-Server yana da matsala (misali, overload).
✅ Yadda ake magancewa:
Duba Laravel error log: tail -f storage/logs/laravel.log
A Laravel, yi:
php artisan cache:clear php artisan config:clear
Idan .htaccess
ne, gyara shi ko a share don a gwada idan shi ne matsalar.
502 – Bad Gateway
🚨 Dalilai:
-Server yana behind a proxy (e.g., Nginx to Apache) kuma akwai matsala wajen isar da request.
-Server ɗinka yana overloaded ko yana da matsala.
✅ Yadda ake magancewa:
Sake kunna Apache/Nginx:
sudo service apache2 restart sudo service nginx restart
Idan Cloudflare kake amfani da shi, tabbatar da cewa server yana aiki da kyau.
503 – Service Unavailable
🚨 Dalilai:
-Server yana da matsala ko yana undergoing maintenance.
-Server yana fama da high traffic ko yana overloaded.
✅ Yadda ake magancewa:
Idan Laravel kake amfani da shi, yi:
php artisan down --message="Maintenance Mode" php artisan up
dan hosting ne, duba idan yana maintenance ko akwai high traffic.
504 – Gateway Timeout
🚨 Dalilai:
-Server ɗinka yana da slow response ko akwai overload.
-Wani proxy (e.g., Cloudflare, Nginx, Load Balancer) yana dakatar da response.
✅ Yadda ake magancewa:
Sake kunna server:
sudo service nginx restart sudo service apache2 restart
Idan kake amfani da Cloudflare, duba idan akwai wani server issue.
🔎 Taƙaitaccen Tebur akan HTTP Errors Da Maganinsu
Code | Ma’ana | Dalili | Magani |
---|---|---|---|
404 | Not Found | Shafi bai wanzu ba | Duba URL, duba routes |
403 | Forbidden | Babu izini | Gyara permissions |
405 | Method Not Allowed | Method ba daidai ba | Duba routes/web.php |
500 | Internal Server Error | Matsala a cikin PHP | Duba logs, share cache |
502 | Bad Gateway | Server overload | Sake kunna server |
503 | Service Unavailable | Maintenance | Jira ko sake kunna server |
504 | Gateway Timeout | Slow response | Sake kunna Nginx/Apache |
wadanan suna HTTP Status wanda suke nuna wani sako ko na dai dai ko na kuskure.
0 Comments